Kebbi: Yansanda sun yi ram da wani dilan miyagun kwayoyi a Ka'oje


Jami'an rundunar yansandan jihar Kebbi reshen Ka'oje sun kama wani mutum dan shekara 35 mai suna Aliyu Abubakar da aka fi sani da suna Falke dauke da miyagun kwayoyi a kauyen Darannan ranar 18 ga watan Mayu da karfe 6:45 na yamma.

A wata takarda da ya fitar amadadin Kwamishinan yansandan jihar Kebbi ranar Alhamis 20 ga watan Mayu. Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya ce, Yansanda sun kama Aliyu wanda ke zaune a Unguwar Bayan Kara a garin Bagudo dauke da wasu kunshi masu kwatankwacin girman komputar Laptop guda 25 dauke da abin da ake zargin busashen ganyen wiwi ne, Da kuma Kwali 20 dauke da kwaya 1000 na Diazepam 5kg kowanne.

An kama kwayoyin ne a jakarsa da ya dauko a kan babur kirar Boxer da yake tukawa lokacin da yansanda suka bincika jakarsa.


Aliyu ya gaya wa yansanda lokacin bincike cewa ya sayo kayakin ne daga wajen wani "Maigida"  a garin Malaville a jamhuriyar Benin.

Ya ce an taba daureshi tsawon shekara 10 a Sokoto sakamakon tu'ammali da irin wadannan kayakin laifi.

DSP Nafi'u ya ce Kwamishinan yansandan jihar Kebbi CP Adeleke Adeyinka Bode, ya bayar da umarnin mika Aliyu Abubakar ga hukumar NDLEA na jihar Kebbi domin gudanar da binciken kimiyya, da kuma gurfanarwa gaban Kotu bisa laifukan da suka jibanci miyagun kwayoyi.

Ya kuma yi kira ga al'umman jihar Kebbi su ci gaba da tsegunta wa jami'an tsaro dangane da bata gari tare da ayyukan miyagu a cikin al'umma.



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN