Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci


Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kudi Naira miliyan 155 ga Ma'aikatan Harkokin Addinin Musulunci na jihar domin siya wa malamai babura a jihar domin su rika yin da'awah, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Alhaji Isah Galadanci ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron Kwamitin Zartarwa na jihar a ranar Alhamis 20 ga watan Mayun shekarar 2021.

Har wa yau, kwamitin ta amince ta fitar da wani kudin fiye da Naira miliyan 196 domin gini da shimfida kwalta tagwayen titi mai tsawon kilomita biyar daga Achida-Tungar Malam-Lambar Kwali a ƙaramar hukumar Wurno na jihar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, "kwamitin ta kuma tattauna a kan shawarwarin da kwamitin da gwamnan ya kafa kan sauya kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari zuwa Jami'ar Ilimi; an kuma amince da kafa kwamitin aiwatarwa."

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN