Mahaifi ya yi wa 'ya'yansa 2 yankan rago saboda dalilan tsafi, duba abin da ya faru


Yansanda sun kama wani mutum mai suna Musilumu Mbwire, bisa zargin kashe 'ya'yansa biyu saboda dalilan tsafi a kauyen Jiira da ke Bbaale a gundumar Kayunga a kasar Uganda.

Kwararrun yansanda sun tone gawar daya daga cikin yaran mai suna Latif Kamulasi dan shekara 7, ranar Talata 13 ga watan Mayu. Sai dai har yanu ba a gan gawar daya yaron mai suna Sahum Baizambona dan shekara 3 ba. Har yanzu yansanda na ci gaba da bincike.

Mahaifin yaran ya gaya wa yansanda lokacin bincike cewa ubangidansa a wajen aiki shi ne ya bukaci ya kashe yaran cewa zai bashi Shi4m wattau kudin kasar Uganda Shilin miliyan 4 da gida.

Ya ce uban gidansa ya ce zai yi amfani da jinin yaran ne domin wata bukata. Sakamakon haka mahaifin yaran ya yi masu yankan rago.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN