An kama "Fatalwa" da ke yi wa jama'a sata cikin dare, duba yadda ta faru


An kama wani matashi da ke sanya bakaken tufafi da ke da hoton Kwarangwam na dan'adam da farin fenti domin ya yi sata a gidajen jama'a.

Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo cewa Matashin yakan sa tufafin da dare, sai ya je gidajen mutane cikin duhun dare, da zarar masu gida sun gan shi sai su tsorata su tsere su bar gidajen su a kasar Zimbabwe.

Sakamakon haka sai matashin ya yi amfani da wannan dama ya sace ababen da ya gan dama a gidajen jama'a.

Dubun wannan matashi ta cika ranar Alhamis 26 ga watan Mayu, kuma an damke shi dumu dumu cikin tufafin "Fatalwa" da yake sanyawa domin ya yi wa jama'a sata.
Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN