Masu Zanga-Zanga Sun Tafi Da Gawarwaki Zuwa Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara


Zanga-zanga ta barke a safiyar ranar Juma'a a garin Zurmi, hedkwatar karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara saboda yawaitar hare-haren yan bindiga da ke kashe mutane a garuruwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mutane da dama sun rasa rayyukansu wasu daruruwan sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren yan bindiga da ya ki-ci ya-ki-cinyewa a garuruwan jihar.

A makon da ta gabata, yan bindiga sun kai hari a wani gari a karamar hukumar Zurmi inda suka kashe fiye da mutane 11.

Mazauna garin sun shaidawa majiyar Legit.ng garuruwa da dama a yankin na fuskantar barazana daga yan bindiga.

Sun dauko wasu gawarwakin sun shiga gari suna zanga-zanga nuna damuwarsu kan hare-haren da yan bindiga ke kai musu.

Wani daga cikin mazauna garin da ya ce sunansa Mustapha ya ce: "Suna hanyarsu zuwa fadar sarki domin gabatar da kokensu.

"Sai dai, Sarkin bai fito ya gana da su ba domin an ce yana cikin gida. Sun yi kone-kone a kafin suka tafi.

"Masu zanga-zangan sun bar fadar sunnan suka hadu a hanyar Gusau zuwa Jibia suka fara fasa motoccin matafiya da ke bin titin.

"Sun kuma fasa gilasan motoccin da aka ajiye a gefen titi."

"Yanzu abubuwa sun dai-daita a yayin da jami'an tsaro ke sintiri a titunan garin domin tabbatar da doka da oda.

"Sannan mutane sun koma sun cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba," in ji shi.

Source: Legit Newspaper

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN