Yanzu yanzu: An kama Lauyan bogi yana tsakar kare shari'a a Kotu


Rundunar yansandan  jihar Ogun ta kama wani Lauyan bogi Dan shekara 50 mai suna Azeez Agboola ranar Laraba 31 ga watan Maris yayin da yake tsakar kare shari'a a gaban Alkali a cikin Kotu.

Lauyan wanda ke zaune a unguwar Oko Afir da ke Badagry a Birnin Lagos, ya bayyana ne a gaban mai sharia B.I. Ilo na Kotun Majistare da ke Agbara domin kare wata sharia da ke gaban Alkalin.

Sai dai yadda ya gabatar da kansa da kuma tafiyar da bayani a gaban Alkali ya haddasa wa Alkalin shakku ko shi cikakken Lauya ne. Sakamakon haka Alkalin ya kira yansanda domin su tantance ko ainihin Lauya ne shi.


Sai dai bayan yan sanda sun gayyace shi kuma suka yi masa tambayoyi, Lauyan ya shaida wa yansanda cewa tabbas ya karanci Law, amma bai ci jarabawan karshe ba sakamakon haka ba a kira shi zuwa makarantar koyon aikin Lauya ba da ake kira Bar.

Yansanda za su gurfanar da shi a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike. A cewar Kakakin yansandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi wacce ta tabbatar da labarin.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN