Kebbi: Gwamna Bagudu ya martaba yan soshiyal midiyan jihar da muhimmin lamari


An gudanar da taron fadakarwa da ilmantarwa kan ka'idodin amfani da kafar sada zumunta na Soshiyal Midiya wajen isar da sako ga jama'a ga Yan Soshiyal midiya a jihar Kebbi ranar Talata 31 ga watan Maris.

Gwamnatin jihar Kebbi ta ma'aikatan watsa labarai na jihar Kebbi ta gudanar da taron na rana days a dakin taro na shugaban kasa da ke Birnin kebbi. Profesa Nura Ibrahim na Jami'ar Bayero da ke Kano, ya gabatar da takardu biyu da lakca kan yadda Yan Soshiyal Midiya za su yi amfani da kafar da suke amfani da su domin kawo ci gaba a jihar Kebbi tare da yin amfani da tsarin wajen cin gaccin alfanu da tsarin ke dauke da shi. 

Profesa ya gabatar da takardu biyu "Social media strategies and tools da kuma Social media as a tool for change and development".


Kazalika Kwararren Dan Jarida Mr Abdallah El-Kurebe, Edita na Jaridar ASHENEWS ya gabatar da lakca da ya ta'allaka kan kiyaye dokoki da ka'idodin rubuta, watsa labarai tare da la'akari da kiyaye yada labaran karya.

El-Kurebe ya gabatar da takardu biyu "Ethics of social media practice da Techniques of writing in social media".

Tun farko, Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya albarkaci taron da manuniya da yancin da ya kamaci amfani da Soshiyal Midiya tare da madogara ga kiyaye tsabtataccen tsari wajen tafiyar da aikin baza labarai cikin al'umma. 


Ya bukaci Yan Soshiyal Midiya na jihar Kebbi su yi amfani da damar da suke da shi su zama Jakadu wajen daukaka darajar jihar Kebbi tare da kiyaye yada labarai da ke iya jawo dakushewar martabar jihar Kebbi.

Alhaji Garba Hamisu, Sakataren dindindin na ma'aikatan watsa labarai na jihar Kebbi ya  wakilci Kwamishinan ma'aikatar. Taron ya sami halartar manyan ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi da manyan yan siyasa a jihar.



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN