Zagin Annabi: Matasa sun kashe wani mutum, sun kone gawarsa gaban Mahaifiyarsa


Fusatattun matasa sun kashe wani mutum mai suna Talle Mai Ruwu, wanda ake zargi da tabin hankali, kuma suka banka wa gawarsa wuta a jihar Bauchi bisa zargin zagin Annabi Muhammadu (SAW).


Jaridar Tribune ta ruwaito cewa, ranar Talata 30 ga watan Maris da rana, matasan sun dira ofishin yansanda a kauyen Sade da ke karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi suka kwce Tall daga hannun yansanda suka yi masa duka har ya mutu daga bisani suka kone gawarsa.


Jaridar ta ce, wani ganau ya shaida mata cewa "Lamarin ya samo asali ne ranar Litinin 29 ga watan Maris bayan wata yarinya ta je Rijiyar da Talle ke samar da ruwa, ta roke shi ruwa don Allah don Annabi, amma cikin fushi sai Talle ya zagi iyayenta har da Annabi.


Wannan lamari ya harzuka jama'a, har zancen ya kai wajen Mai gari, bisa wannan dalili Mai gari ya kai Talle wajen yansanda ranar 29 ga wata kuma ya kwana rufe a ofishin yansanda". 

Majiyar ta ce "Bayan labarin ya bazu ko ina a cikin kauyen, ranar 30 ga wata da tsakar rana, fusatattun matasa sun yi gangami suka je ofishin yansanda a kauyen suka kwace Talle daga wajen yansanda da karfin tsiya, suka yi masa dukan ajali kuma suka dinga jan gawarsa a kasa, daga bisani suka kai gawarsa gaban gidansu inda suka banka wa gawar wuta a gaban mahaifiyarsa wacce tsohuwa ce mai yawan shekaru".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN