Fiye da gidaje 100 sun kone, tare da mutane da dama yayin da wata motar tanka dauke da man fetur ta fadi ta yi bindiga ta kama da wuta a garin Oshigbudu da ke karamar hukumar Agatu a jihar Benue ranar Lahadi 18 ga watan Aprilu da rana.
Motar tankar ta fito daga Oweto kan hanyarta ta zuwa Otukpo sai moyar ta kwace wa direba a dai dai magamar hanyar Oshigbudu da Obagaji ta je ta fadi.
Sakamakon haka man fetur da ta dauko ya malale zuwa gidajen jama'a kuma ya kai wani gidan mai da ke kusa. Daga bisani aka jiyo karar fashe mai karfi, sai gobara ta tashi nan take.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Agatu Mr, John Ikwulono ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bukaci taimakon gaggawa daga hukumomin bayar da agajin gaggawa da kungiyoyin agaji masu zaman kansu. Ya ce har zuwa dare ranar Lahadi gobarar na ci gaba da lakume gidajen jama'a. Ya ce jama'a da yawa sun mutu a gobarar.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari