An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram


Wasu sojoji da aka kama yayin binciken masu daukan nauyin yan Boko Haram sun bayyana sunayen wasu fararen hula da suke aiki tare da su a cewar majiyoyi, rahoton Daily Trust.

An kama sojojin ne bayan bincike mai zurfi da aka yi kan alakar da ke tsakanin yan Boko Haram da jami'an sojoji, da suka taimaka musu wurin zagon kasa kan yakin da ake yi na kawo karshen ta'addanci a Nigeria.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da bincike kan wadanda suke daukan nauyin yan ta'adda da masu hada kai da Boko Haram.

Wani babban jami'in tsaro mai binciken sirri ne ka jagorantar binciken tare da babban janar na soja d wasu ma'aikata daga hukumomin binciken sirri.

Majiyoyi da dama sun sanar da majiyar Legit.ng cewa Hukumar Binciken Sirri na kasa, DIA tare da hadin kan DSS, NFU da babban bankin kasa CBN ne ke binciken.

A halin yanzu an kama sojoji 20 da ake zargi da hannu cikin lamarin kuma suna tsare a Borno.

"An kama kimanin 20 daga cikinsu suna tsare a Borno. A yayin binciken sun bada bayanai masu yawa ciki har da sunayen wasu fararen hula da suke aiki tare da su inda suka aka kama su," majiya ta shaidawa Daily Trust.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar sojoji, Manjo Jana Mohammed Yerima ya ce ba shi da masaniya kan kama sojoji da ake zargi suna hada kai da yan Boko Haram.

Ya kuma ce hukumar yan sandan farar hula, DSS, ya kamata a yi wa wannan tambayar domin su ke kula da batutuwan da suka shafi kama masu daukan nauyin ta'addanci.

Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS, a yayin da aka tuntube shi a ranar Juma'a ya ce zai yi bincike kafin ya yi tsokaci kan batun. Amma bai bada bayanin ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton.

Bai kuma amsa kira da sakon kar ta kwana da aka yi ta tura masa ba.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN