An shiga firgici a layin Douglas da ke Owerri babban birnin jihar Imo a yayin da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suke kokarin afkawa yankin Hausawa da ke unguwar a ranar Litinin.
Daily Trust ta ruwaito cewa an yi ta jin karar harbin bindiga a daren ranar Litinin a yayin da sojoji da yan sanda da aka tura unguwar ke fafatawa da yan bindigan.
Wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane ke gudu don kare ransu sakamakon musayar wutar.
An gano cewa yan bindigan sun tafi bayan sun gaza jure luguden wuta da jami'an tsaron ke musu.
Babban mashawarci na musamman ga gwamna Hope Uzodinmma a kan harkokin yan Arewa da marasa galihu, Hon Suleiman Ibrahim Suleiman ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya bayyana cewa jami'an tsaron sun dakile harin da yan bindigan suka kai.
Ba a yi nasarar ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ebonyi, SP Orlando Ikeokwu ba a kan batun.
Source: Legit.ng
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI