An bizine gawar DPO na yansandan karamar hukumar Sakaba SP Jimoh Abdullahi tare da yansanda biyu na ofishinsa da Yan daban daji suka kashe a karamar hukumar Sakaba da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.
FPO na daga cikin yansanda guda Tara da Yan sa Kai uku da yan daban daji suka kashe ranar Lahadi 25 ga watan Aprilu, sakamakon musanyar wuta da bindigogi tsakaninsu da Yan daban daji.
Jami'an yansanda da suka rasa rayukansu sun hada da Inspector Crime Aliyu Ibrahim, Inspector Nathan Langa, Inspector Suleiman, Inspector Simon Linglong, Inspector Samson Stephen, Inspector Borniface, Sgt. Ajimomo, Sgt. Jonathan James, da kuma Yan sa Kai Umaru Dantaru, Audu Fesse da Arage Yadga.
Dukkansu suna daga cikin ayarin yansandan kwantar da tarzoma Mopol da aka tura daga Zuru domin Kai agaji wajen kare rayuka da dukiyan jama'a a karamar hukumar Sakaba sakamakon farmakin Yan daban daji kan al'umman yankin.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka