Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Tarayya Dake Ebonyi Wuta


Yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun cinna wa Babban Kotun Tarayya na Abakaliki, Jihar Ebonyi, yankin Kudu maso Gabashin Najeriya wuta.

Ginin yana kan babbar hanyar Enugu/Abakaliki, daura da ofishin jam'iyyar PDP ta jihar.

Wasu ‘yan bindiga ne sukai amfani da bama-bamai suka kai harin a ranar Talata, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilin Premium Times.

Gobarar wadda ta fara da sanyin safiyar yau ta shafi dakin karatu da kuma ofishin tsaro na kotun.

Sai dai an ce daga baya jami’an kashe gobara sun tattara zuwa wurin don kashe gobarar kafin ta sake yin barna.

Babu wani wanda ya mutu a harin wanda ya lalata bayanan kotu da dama a dakin karatun.

Kakakin yan sanda a jihar, Loveth Odah, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce maharan sun zo da yawansu don kai harin.

Karin bayani nan gaba...

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN