Kungiyar malaman addinin kirista na 'Forum of Christian Bishops and Clergy Council' ta nuna goyon bayan ta ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan matsayarta game da zargin da ake yi wa ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dr Isa Ali-Pantami.
Kungiyar ta sanar da hakan ne yayin wani tattaki na goyon baya da ta yi a Unity Fountain Abuja, inda ta ce wadanda ke zargin wasu tsirarai ne a kasar da basu son sauye-sauyen da ministan ke yi.
Malaman addinin na kirista sun fito rike da takardu masu rubutu da ke nuna goyon baya da ga gwamnatin Buhari da rokonsa ya cigaba da hada kan yan kasa.
Har wa yau, kungiyar ta ce ta yi tattakin ne na zaman lafiya domin jadada bukatar zaman lafiya da hadin kai a kasa.
Bishop Abel King, jagoran masu tattakin ya ce ya zama dole su fito su bayyana matsayarsu saboda irin zargin da ake yi wa Mr Pantami.
"Shugaban kasa bisa hikimarsa ya nuna cewa Nigeria ne ke gabansa kuma zai cigaba da hada kanmu sannan ba zai bari masu son kai su rude shi ba ko tilasta shi," wannan abin yabo ne in ji Bishop Abel.
Bishop Abel ya cigaba da cewa ya kamata mutane su dena la'akari da banbancin addini, kabila ko yanki idan za su dauki mataki sai dai su mayar da hankali kan abin da zai kawo cigaba a kasa.
Kazalika, ya gargadi mutane kan furta kalaman da ka iya tada zaune tsaye a kasar.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI