Yadda aka rataye Limami, magidanci ya mutu a bayan Kara, Birnin kebbi


Wani magidanci mai suna Abubakar Zaki Tari ya rasu bayan an sami gawarsa rataye da igiya a Kemis da yake aiki, wanda ke kofar gidansa da ke kan titin Yan tumatir a unguwar bayan Kara da ke garin Birnin kebbi da ke Kebbi ta tsakiya a Masarautar Gwandu a jihar Kebbi ranar Juma'a 9 ga watan Maris da dare.

Majiya da ke kusa da iyalin marigayin ta ce marigayin wanda aka fi sani da Dr Tari, ma'aikacin sashen tiyata ne da ke Asibitin Tarayya ta Federal medical center FMC da ke Birnin kebbi. Kuma daya daga cikin Kwararrun sashen tiyata da ake takama da su a FMC Birnin kebbi kafin rasuwarsa. Lamari da ya sa ya shahara kuma sunansa ya yi fice a wannan aikin a Birnin kebbi.


Wani kanin marigayin mai suna Aliyu Umar, ya ce " Mahaifiyar marigayin ta je ta same ni a wajen barci na da safe, ta ce in tashi in nemo mata Alhaji a Masallaci inda yake bayar da Sallah, an yi neman shi ba a gan shi ba.

Na je na tambaya a Masallaci inda yake bayar da Sallah, wani ya ce min shi ya makara wajen zuwa Masallaci bai san wanda ya bayar da Sallah ba. Sai aka kira Naibin Limami wanda ya tabbatar cewa shi ne ya bayar da Sallah domin Liman Alhaji Abubakar bai zo ba.


Sai na dawo gida na gaya masu cewa an tafi Masallaci baya nan. Sai na gan Kemist inda yake aiki an bar kofa a bude. Sai na je na leka, sai na gan shi. Sai na ruga na bugi kofar gidan makwabcinsa wanda yake a rufe, amma sai kofar ta bude. Sai na gaya mashi. Sai muka ruga, da ni da makwabcinsa da matarshi daya muka je wajen.

Abin da na sani kenan, daga nan na bar makwabcinsa tare da matarshi guda suna kururuwa. Cikin rudani na tafi can waje gidan Malam Usman. Ko da na dawo na sami jama'a sun yi yawa. 


Alhaji makwabcin marigayin, lokacin da na Kira shi ya sa rigarsa ya je ya leka ya gan marigayi a rataye da igiya, sai da ya fadi saboda tsananin kaduwa ! ".
 
Malam Aliyu Umar, ya ce marigayin Alhaji Abubakar Zaki dan asalin garin Tari a karamar hukumar Gwandu, Limami ne, Malami mai wa'azi, gwani kuma kwararre a harkar tiyatar fida a Asibitin FMC Birnin kebbi, hazaka da ya kai shi ga fice a wannan fanni, ya zauna lafiya da kowa, makwabta, wajen aiki, hulda da muamala mai kyau.


Haziki wanda ke son dogaro da kansa ta hanyar yin sana'a bayan aikin gwamnati. Ya rasu ya bar mata biyu da yara 7 maza 9 mata.

Wannan lamari ya haifar da fargaba a tsakanin jama'a a garin Birnin kebbi, tare da fatar Allah ya tona asirin wanda, ko wadanda suka yi masa wannan danyen aiki, a cewar wani abokinsa da yake kofar gidan marigayin tare da jama'a da ke kofar gidan don amsar gaisuwa da tausayawa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN