Akwai yiwuwar farashin fetur ya rage tsada bayan darajar danyen mai ya ragu


Rahotanni daga jaridar Punch ta rahoto cewa man da Najeriya ta ke saida wa a kasuwar Duniya ya na cigaba da rage daraja a halin yanzu.

A ranar Alhamis, 8 ga watan Afrilu, 2021, farashin gangar man ‘Brent’ ya sake yin kasa a kasuwa.

Rahotanni daga kasar waje sun tabbatar da cewa gangar man Brent ya tashi ne a kan fam $62.92 da kimanin karfe 6:00 na yammacin jiya Alhamis.

Idan aka kamanta farashin da abin da aka saida man na Najeriya a tsakiyar makon nan, kowace ganga ta rasa $0.24, kusan N100 a kudinmu na gida.

Masana da ‘yan kasuwa su na ganin cewa idan aka cigaba da tafiya a haka, za a kai lokacin da dole farashin man fetur ya ragu a gidajen man Najeriya.

Masu kasuwancin mai a Najeriya sun shaida wa jaridar Punch cewa farashin zai fi tasiri idan gwamnatin tarayya ta zare hannunta daga harkar.

Tun a watan jiya da farashin gangar mai ya doshi $70, har yanzu bai sake tashi ba. A kullu-yaumin farashin man fetur fadu wa kasa yake yi a kasuwa.

A watan Maris ne gangar mai ya yi tashin da bai taba yi ba a cikin sama da shekara guda. Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, ganga ta tashi a kan N24, 000.

Babban jami’in kungiyar IPMAN, Cif Chinedu Ukadike, ya tabbatar da cewa watakila farashin fetur ya sauka a gidajen mai idan gangar mai ya tsaya a haka.

Wannan shi ne ra’ayin shugaban kungiyar Petroleum Products Retail Outlets Owners, Mista Billy Gillis-Harry, ya na mai ba gwamnati shawara ta cire hannunta.

Kwanaki kun ji cewa gwamnatin tarayya na shirin kara farashin dakon man fetur. Rahotanni sun bayyana cewa za a rage kudin kowane lita daga N7.51 zuwa N9.11

Sakataren hukumar da ke tsaida farashin man fetur na kasa, Alhaji Ahmed Bobboi, ya bada wannan sanarwar bayan wani taro da aka yi da masu motocin haya.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN