Type Here to Get Search Results !

Matsalar tsaro da yan bindiga a Kebbi: Bagudu ya dauki muhimman matakan tsaro


Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce Gwamnati za ta dauki matakin gaggawa domin tabbatar da tsaron lafiyar jama'arta.

Ya ce Gwamnatin jihar za ta yi aikin ganin an ci ma wannan nassara tare da hadin gwiwa da jami'an tsaro, Sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.

Bagudu ya yi wannan jawabi ne ranar Asabar lokacin ziyara da ya kai kauyen Mugaba da ke karamar hukumar Danko-Wasagu, bayan harin Yan bindiga kan al'umman wanan yankin, lamari da ya yi sanadin mutuwar wasu bayin Allah da kuma jami'an tsaro.

Gwamnan ya ce zasu kara kaimi wajen ganin an kara turo yansanda a yankin domin tabbatar da tsaron rayukan jama'a.

Bagudu ya ce "Idan baku manta ba, an kara yawan jami'an tsaro guda 200 ba da dadewa ba, tare da wasu matakan tsaro da ba za mu fada ba a nan" 

Ya ce Gwamnati bata haramta kungiyar Yan Sakai ba kai tsaye saboda tsari ne mai kyau. Duk da yake wasu bata gari sun kutsa cikin tsarin. 

Mu yi aiki tare, masu hakuri da juna, masu zaman lafiya da bin doka". 

Gwamna Bagudo ya saurari wasu jama'a a kauyen Magaba, wadanda ganau ne ba jiyau ba, yadda abin ya faru lokacin da yan bindigan suka shigo kauyen.

Liman Abdullahi Baba, Aminu Dadu, Adamu Magaji, Pastor Emmanuel Gavo duk sun gaya wa Bagudu yadda Yan bindigan da suka zo kan babura suka kashe mutum 6 a kauyukan Gulumbo, 5 a Magaba da 3 a Matseri.

Sun ce Yan bindigan sun yi wasoson kayakin cikin shaguna suka kwashe abin da suke iya daukewa, musamman wayoyin salula da dabbobi.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies