Ta kulle tagwayenta masu shekara 3 har kwana 3 a daki ba tuwo ba ruwa


Rundunar yansandan jihar Ekita ta kama wata mata mai suna Joy Fatoba, sakamakon kulle tagwayenta masu shekara 3 a cikin daki har tsawon kwana 3 ba tare da basu abinci ko ruwan sha ba.

Kakakin rundunar yansandan jihar Ekiti Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Litinin 5 ga watan Maris. Ya ce yansanda sun ceto yaran kuma sun kai su Asibiti domin samun kulawan Likitoci .


Abutu ya ce ranar Lahadi 4 ga watan Aprilu yansanda sun sami kira daga karamar hukumar Igbara-Odo, Ekiti ta kudu maso yamma a jihar Ekiti cewa wata mata ta kulle yaranta a cikin daki har tsawon kwana 3 ba tare da basu abinci ko ruwan sha ba.


Ya ce matar ta yi barazanar cewa za ta kashe yaran idan aka tilasta ta bude kofar.


Sai dai rahotanni sun ce matar ta yi zargin cewa tun lokacin da ta dauki cikin yaran, mahaifinsu ya yi tafiyarsa, har ta haihu bai dawo ba. Ta ce yanzu haka lamurra sun yi mata tsauri tare da kuncin rayuwa sakamakon rashin ci gaba a sana'ar kitso na Saloon da take yi wanda da shi ne take samun kula da yaran.


Kazalika rahotanni sun ce ala tilas yansanda suka kai yaran Asibiti bayan an bude daki da mahaifiyarsu ta kulle su domin sun kasa tsayuwa a kafafunsu sakamakon yunwa da kishin ruwa.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN