Postan "Buhari must go" a jihar Arewa, yansanda sun kama mutum 2


Rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi ta cafke wasu mutane biyu da ba a bayyana sunayensu ba da ake zargi da shirin fara kamfen din bata sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a Lokoja, babban birnin jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kwamishinan yan sanda na jihar Kogi, Ayuba Edeh, ya tabbatar da kamun a ranar Litinin, 5 ga watan Afrilu.

Legit.ng ta tattaro cewa an kama mutanen biyu da misalin karfe 2:30 na tsakar dare yayin da suke zana gine-gine da lika fastoci dauke da rubutun: 'Dole ne Buhari ya tafi'.

Edeh ya bayyana cewa yayin da ‘yan kasa ke da‘ yancin yin zanga-zanga, dole ne a yi hakan ta hanyar da ta dace ba tare da tunzura jama’a ba, Daily Trust ta kuma ruwaito.

Shugaban 'yan sandan ya kara da cewa da samarin ba za su yi zanga-zanga cikin dare ba, yana mai cewa ba za a iya kiran zanen bango da manna fastocin adawa da Buhari a matsayin zanga-zangar lumana ba.

Gwamnatin Kogi ta mayar da martani

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya yaba wa matasan, yana mai cewa su ne suka cafke masu zanga-zangar kin jinin Buhari suka mika su ga ‘yan sanda.

Fanwo ya ce jihar Kogi ta kasance matattarar shugaba Buhari mai karfi, yana mai zargin cewa an bugo fastocin adawa da Buharin ne a jihar kudu maso kudu.

Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen inganta rayuwar mutane kuma ba za ta yarda kowa ya yi siyasar raba kawunan jama'a ba.

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shekaru bakwai kenan da kafa jam'iyyar APC amma har yanzin ba ta zama haÉ—aÉ—É—iyar jam'iyya ba.

Gwamnan ya bayyana jam'iyyar da cuÉ—uwar jam'iyyun siyasa da suke faman ganin sun zama jam'iyya É—aya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Ganduje ya yi wannan jawabi ne a wani taro da kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin APC na yankin arewa maso yamma ya shirya a jihar Kano.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN