Gurgu ya hargitsa gangamin APC, ya yi wa Shugaban karamar hukuma ihun ‘Ba mu so’


Wani bidiyo ya na zagaye kafofin yada labarai inda aka wani Bawan Allah ya na yi wa shugabannin jam’iyyar APC ihun bore da rana-tsaka.

Wani wanda ake kira Kwankwason Twitter shi ne ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Twitter.

Yayin da ake shirin kiran shugaban karamar hukuma ya yi jawabi, sai wannan mutumi da gurgu ne ya zaburo, ya fara yi masa ihun cewa ba su son shi.

Wannan mutum gurgu ne wanda yake tafiya da sanduna, amma ya yi ta-maza ya shigo tsakiyar taro, ya na sukar shugaban karamar hukumar mai-ci.

Za a ji gurgun ya na cewa: “Karya ne, ba mu yi! Me ya yi mana wannan! Makaryaci ne wannan. Babu abin da ya yi mana. Ba mu so. Ba mu son shi…

Alamu sun nuna cewa wannan lamari ya faru ne a lokacin kaddamar da ‘dan takarar shugaban karamar hukuma wanda ya ke mulki a jam’iyyar APC.

Mabiya shafukan sada zumunta na zamani sun bayyana cewa wannan abin kunya ya faru ne a garin Tudun-Wada, karamar hukumar Zaria, jihar Kaduna.

Jam’iyyar APC mai mulki ce ta ke shugabancin karamar Zaria, kuma ana sa ran za ayi zaben shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli a watan Yuni.

A cewar wani Bawan Allah, sunan wannan gurgu Ahmad, wanda ake kira da ‘Dudu’ a Tudun-Wada.

Wasu wanda su ka san wannan gurgu sun ce fitaccen ‘dan takife ne maras tsoro, kuma da ace ya na da kafafu, da watakila sai ya yi gigin marin ‘yan siyasa.

Kwanaki kun ji gwamnatin jihar Kaduna ta ce idan aka kama mutum ya yi magana da masu garkuwa da mutane da nufin biyan fansa zai dandana kudarsa.

Iyayen yaran da aka sace a Afaka sun yi tir da matakin da Gwamnatin Kaduna ta dauka, sun nuna a shirya su ke su biya kudi domin a fito masu da 'ya 'yansu.

Source:  Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN