Sojoji sun kashe Abu Aisha da wasu manyan kwamandojin ISWAP 17 a Damasak


Dakarun Sojojin Nigeria sun kashe babban kwamandan ISWAP, Bukar Gana Fitchmeram (aka Abu A'isha) da wasu mayakansa da suka zo ramuwar gayya a Damasak amma suka haɗu da ajalinsu hannun sojoji a ranar Alhamis.

Rundunar Sojin ta ce ƴan ta'addan sun gamu da karshen su a yayin da suka kai hari bayan kashe manyan kwamandojin ISWAP 12 a ƙaramar hukumar Mobbar sakamakon hare-haren ƙasa da sama da sojojin suka shafe yi na kwanaki 7.

Kakakin soji, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ne sanar da hakan ta shafin Twitter na rundunar a ranar Juma'a.

A baya an ruwaito cewa ƴan ta'addan sun kashe wasu sojoji sun kuma lalata ginin Majalisar Dinkin Duniya yayin harin da suka kai Damasak amma Yerima, a ranar Juma'a ya ce an kashe manyan kwamandojin ISWAP da jiragen yaki yayin harin.

Ya yi wa sanarwar laƙabin 'Yadda manyan kwamandojin ISWAP suka gamu da ƙarshen su yayin da suka dawo ɗaukan fansa a Damasak.'

Sanarwar ta ce, "Hare-haren sama da aka kai a Tudun Wulgo, Zafi, da Tumbun Alhaji, Kusuma, Sigar a Ngala da Arijallamari a Abadam, Marte a ƙaramar hukumar Ngala ya yi sanadin kashe manyan kwamandojin ISWAP.

"Kwamandojin da aka kashe yayin harin saman sun hada da Mohammad Fulloja, Ameer Mallam Bello, Ba'a kaka Tunkushe , Abu Muktar Al-Ansari, Ameer Abba Kaka, Abu Huzaifa, Ameer Modu Kwayem, yayin da Goni Mustapha wanda shine babban limamin ISWAP ya tsira da raunin harsashi."

Rundunar sojojin ta kara da cewa hare-haren sama da ƙasa da aka kai a ranar 6 ga watan Afrilu ya yi sanadin mutuwar manyan kwamandojin ISWAP biyu ciki har da Abu-Rabi da Muhammed Likita da masu tsaronsu a kusa da Kusuma, Sigir a ƙananan hukumomin Ngala da Arijallamari, Abadam.

An kuma lalata wuraren da ƴan ta'addan ke ajiye makamansu yayin samamen da dakarun Operation Lafiya Dole suka kai.

A daren ranar 10 ga watan Afrilu, Yerima ya yi bayanin cewa dakarun Sojojin sun ritsa wasu kwamandojin yan ta'addan uku a kusa da Wulgo/Logomani kusa da iyakar Kamaru yayin da suke kokarin satar shanun mutanen yakin, wadanda aka kashe sune Ameer Umar, Abu Ubaida da Abu Salim.

A cewarsa, wannan illar da aka yi wa ƴan ta'addan ya saka sun fara kai hare-hare suna satar abinci da magunguna don kulawa da yan uwansu da suka jikkata.

Har wa yau, rundunar sojin ta ce a ranar 11 ga watan Afrilu, sojojin sun halaka wasu ƴan ta'addan a cikin motocci masu bindiga 5 a Damasak.

Ya ce an wasu daga cikin ƴan ta'ddan sun samu shiga garin na Damasak inda suka kone gine-gine suka sace kaya kafin suka tsere.

Wannan ba shine karo na farko da aka kai hari Damasak ba amma duk da hakan sojojin na cike da izza a yakin da suke yi da ƴan ta'addan duk da akwai ƴan leken asiri da ke sanar da ƴan ta'addan inda sojojin suke.

Source: Legit Newspapers


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN