Type Here to Get Search Results !

Sharhin Fim Din ‘Kawaye


Suna: kawaye.
Tsara labari: Ibrahim Birniwa
Kamfani: Ramlat Investment.
Daukar Nauyi: Hafsat Idris.
Shiryawa: Naziru Dan Hajiya.
Bada Umarni: Ali Nuhu.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Ali Nuhu, Sani Danja, Hafsat Idris, Aisha Humaira, Hajara Usman, Rahama M. K, da sauransu.

Fim din kawaye, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wasu kawaye guda biyu wato Fatima (Hafsat Idris) da Kuma Rumasa’u (A’isha Humaira). kawaye ne dai a Jami’a. Rumasa’u watarana ta kawowa Fatima korafin cewa saurayinta Yusuf (Ali Nuhu) ya watsar da ita ya daina neman ta gaba daya, kuma ya daina kula ta gaba daya. A karshe ta nemi ta raka ta Abuja domin su je gurun Yusuf domin a yi sulhu. Sai dai Fatima da farko ta nuna kin amincewar ta a kan tafiya Abujar saboda gudun kar ta hadu da saurayinta wanda zai aure ta wato Sageer( Sani Danja).

Da su ka isa Abuja sai su ka tsara cewa Fatima ita ce za ta je ta samu Yusuf ita kadai, saboda idan ya gane su na tare da Rumasa’u to ba zai saurare su ba. Fatima sun hadu da Yusuf, shi ne ya je ya kama mata Otel domin idan ta gama abinda ta ke sai ta kwana a nan. Abinda Fatima ta ji tsoro tun farko sai da ya faru domin kuwa Sageer ya ganta lokacin da su ka shigo Otel da Yusuf, sai dai su ba su ganshi ba. Ya yi kokari ya je ya same ta sai sun bace masa. Bayan Yusuf sun gama tattaunawa da Fatima, ya fada mata duk abinda ya sa ya rabu da Rumasa’u na munanan halayenta, da zai tafi sai ya bata kudi dubu 200.

Daga nan ne kuma sai rikici ya balle a tsakanin Fatima da Rumasa’u, saboda ta na zargin cewa Fatima soyayya su ke da Yusuf a boye. Fatima abin ya yi mata ciwo sai ta bata kudinta ta yi tafiyar ta. To bayan sun rabu sai Rumasa’u ta kirawo Babar su Fatima ta ke fada mata ai Fatima ta tafi yawon banza Abuja gurun saurayinta. Nan ta kara rikitawa Fatima lissafi. Sannan shi ma Sageer ya aiko gidan su Fatima a ka karbar masa kayan lefensa da niyar ya fasa aurenta, tunda har ya ganta da wani a Otel.

A Karshe dai bayan an gane tuggun da Rumasa’u ta kullawa Fatima domin ta bata ta a gidansu, an gane ba laifin Fatima bane. A karshe Yusuf ya amince ya aure ta, saboda halaye na gari da ya gani a tattare da ita.

ABUBUWAN YABAWA

  1. Fim din ya dace da sunansa.
  2. Fim din ya nuna muhimmancin gaskiya, domin gaskiyar ce ta zama riba ga Fatima.
  3. Ba a samu matsalar sauti ko hotu a cikin fim din ba.
  4. Labarin fim din bai yanke ba tun daga farko har karshe.

KURAKURAI

  1. An nuna su Fatima da Rumasa’u ‘yan makaranta ne amma babu wata alama da za ta tabbatar da hakan.
  2. An nuna ana binciken Sageer a kan zargin kisa, amma ko kadan mai yin zargin da kuma inda a ke tuhumar Sageer din,a babu wata alama da za ta nuna dan sanda ne.
  3. Har fim din ya kare ba a nuna an wanke Sageer daga zargin da a ke masa ba, kuma ba a nuna an tabbatar da zargin a kansa ba.

KARKAREWA

fim din kawaye, fim ne da ya samu aiki mai kyau. Kuma ya yi nasarar isar da sakon da a ke da bukatar ya isar. Jaruman fim din sun yi kokari sosai. Kuma labarin fim din ya tsaru.

Rahotun Leadershipayau


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies