Ina alfaharin ni’imar da Allah ya yi mini a harkar Fim – Rahama M K


Rahama Mukhtar Sulaiman, wadda aka fi sani da sunan Rahama M K ko kuma Fulanin Bawa Mai kada a cikin shirin Kwana Casa’in. Fitacciyar jaruma ce da a yanzu take haskawa saboda rol din da ta taka a matsayin ta na matar Gwamna a cikin shirin Kwana Casa’in, irin dacewar ta da rol din ne ya sa ta samu karbuwa a wajen masu kallon shirin wadda a hakan ya zamar da ita babbar jarumar da ta ke sahun gaba a wannan lokacin.

Domin jin tarihin rayuwar ta da kuma yadda ta samu kan ta a cikin harkar fim, wakilin mu a Kano ya tattauna da ita don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.

Rahama M K. To da farko dai suna na Rahama Mukhtar Sulaiman wadda aka fi sani da Rahama M K, Kuma an haifeni a shekarar 1987 na yi Makarantar firamare a ABU Zaria Staff School. Na fara Sakandare a GSS Shika na karasa a Eleganzer International School da ke Kano. Na yi Diploma a Annur Islamic Institute ABU Zaria, kuma na yi aure ina da yara biyu a Jos. Kuma ina aiki a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano.

To ko ya ya aka yi kika samu shiga harkar fim?

Yadda na samu shiga harkar fim dai shi ne akwai wata ‘yar uwa ta wacce ta ke harkar fim Aisha Tafida Gombe wadda ganin ta ne a cikin fim ya sa na fara sha’awar shiga harkar, kuma na fara harkar fim din Hausa a 2013 in da na fara da fim din Aminai, sai Nisan kiwo da kuma wani fim Ka ci amanata. Amma dai tun ina karama ina da sha’awar harkar sai dai ita Aisha ta karfafa mini gwiwa ne, don haka na taso ina sha’awar harkar fim kuma na gamsu da za ka iya isar da sako ka kuma ilmintar sosai. A bangaren wannan shi ne abin da ya sa na shiga kuma na yarda cewar sana’a ce shi ya sa na fara.

To ya aka yi kika samu shiga shirin Kwana Casa’in ?

E akwai Abdulkarim Papalaje, shi ne wanda na ke gani a matsayin Uban gidana tun da Usman Mu’azu ya hada ni da shi a matsayin Manaja na shi ya sanar mini za a fara tantance masu son shiga aikin kwana Casa’in din, don haka ta hanyar sa ne na samu shiga cikin shirin Kwana Casa’in kuma na yi sa’a na samu wannan rol na Matar Gwamna wadda a yanzu duk duniya aka sanni da shi.


To ya kika ji a matsayin ki na jaruma da kika hau rol din Matar Gwamna?


Gaskiya na ji dadi sosai na kuma godewa Allah da ya sa na samu wannan rol din kuma ina alfahari da shi.domin yadda mutane su ke girmama ni da kuma yadda su ke kallo na a matsayin babbar mace mai aji shi ya fi burge ni don haka ina jin dadi sosai.

Da ya ke yanzu kin zama babbar Jaruma za a iya cewa burin ki ya cika?


Alhamdulillah buri na ya cika sai dai godiya ga Allah, a Koda yaushe ina Kara gode masa Alhamdulillah. Domin kuwa a dalilin fim din na yi gida na yi. Mota, aikin Hajji na ke da burin na je a yanzu in sha Allahu. Don a yanzu ko’ina na je wucewa mutane na farin ciki da zuwa na saboda da sun ganni ko’ina na wuce daga me cewa Matar Gwamna sai masu cewa Fulanin Bawa Mai kada, ina alfahari da Ni’imar da Allah ya yi mini Alhamdulillah.


Menene sakon ki na karshe ga jama’a?
To sako na dai bai wuce na yi wa masoya na godiya ba saboda irin kaunar da su ke nuna mini domin duk wani abu da na zama a rayuwa ta sanadin kaunar da su ke yi mini ne, don haka nagode sosai Allah ya bar mu tare da su.

Rahotun Leadershipayau


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN