Wani faifen bidiyo da ke yawatawa a shafukan intanet ya tayar da kura bayan ya nuna wasu samari da ake zargin yan "Yahoo boys" ne su uku suna wanka a cikin Makabarta.
Bidiyon ya nuna samarin daure da jar kyalle a kwankwason su suna wanka a cikin Makabarta.
Wani abin mamaki shine yadda daya daga cikin samarin yana furta kalaman kirayen aljanu ko tsafi a bakin wani Kabari, yayin da sauran samarin biyu ke ci gaba da yin wanka.
Bisa ga alamu, wani ne ya labe a wani guri ya dauki cikakken bidiyon lamarin.
Bidiyon ya nuna yadda samarin suka ajiye sabulu da suka yi wanka da ita a kan wani Kabari, kafin su ketare katangar Makabartar su tsere.
Kalli bidiyo:
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari