Type Here to Get Search Results !

Da gaske an harbe ɗan Idriss Deby?


Kafofin yaɗa labarai na Chadi sun ba da rahotanni masu karo da juna game da zargin harbe-harbe a fadar shugaban kasar Chadi a N’Djamena kan wata taƙaddama tsakanin iyalin marigayi Idriss Déby game da naɗin ɗansa Mahamat Idriss Déby Itno a matsayin wanda ya gaji mahaifinsa. BBC Hausa ta ruwaito.

A wasu jerin saƙwanni daga shafin Twitter na kafar Tchadinfos ta ambato majiyoyi da dama da ba ta bayyana suna ba musanta cewa an yi harbe-harben.

Amma a nata ɓangaren kafar Toubou ta ambato majiyoyin tsaro da ke cewa Mahamat ya ji rauni a harbe-harben sakamakon saɓanin da aka samu.

Tchadifos ta ce "Shugaban riƙon kwarya yana raye kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Babu wani harbi da aka yi kuma babu wani saɓani tsakanin Mahamat da ɗan uwansa Zakaria."

Marigayi Déby yana da ƴaƴa da yawa, ya yi aure da yawa, kuma yana da yara da ba a san yawansu ba.

A nata labarin kuma Jaridar Alwahida Info mai goyon bayan gwamnati ta ce an ji ƙarar harbin bindiga a Ati, da ke nisan kilomita 378 da gabashin N'Djamena bayan fursunoni sun yi ƙoƙarin tserewa .

Amma Jaridar ta ce “ƙura ta lafa” bayan tura sojojin a yankin.

An sanar da mutuwar Idriss Deby a ranar Talata inda aka ce ya mutu sakamakon raunika da ya samu a filin dagaImage caption: An sanar da mutuwar Idriss Deby a ranar Talata inda aka ce ya mutu sakamakon raunika da ya samu a filin daga.

Ƴan adawa na son a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta farar hula a Chadi

Jam'iyyun adawa a Chadi sun yi kira da a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da farar hula za su jagoranta, inda suka yi Allah wadai da abin da suka kira juyin mulki, bayan rasuwar shugaban ƙasar Idris Deby a jiya Talata.

Bayan dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, sojojin kasar sun ce ɗan Idris Deby Mahamat ne zai jagoranci kasar har lokacin da za a gudanar da zabe.

A wata sanarwa, kusan ƙungiyoyin adawa 30 ne suka yi kira ga jama'ar kasar da kada su goyi bayan abin da suka kira matakin karya doka da gwamnatin riƙon ƙwarya ta soji ta ɗauka.

A yanzu dai an sanar da sake buɗe iyakokin ƙasar da aka rufe da kuma sassauci kaɗan ga dokar hana fita ta dare.

Ƴan adawar kuma sun yi gargaɗi ga ƙasar Faransa da ka da ta tsoma baki a harkokin siyasar ta Chadi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies