Kebbi: Da sunan Kauran Gwandu, kungiyar KAGAF ta yi abin alhairi ga matasa 320

Kungiyar Kauran Gwandu Advocacy a jihar Kebbi, ta kaddamar da  rabawa matasa kyautar JAMB FORM, lamari da ya samar wa matasa 320 kyuatar wadannan form ranar Laraba 21 ga watan Aprilu.

Shugaban kungiyar a jihar Kebbi Mansur Sarki Gwandu ya ce

"Wannan kungiya na Kauran Gwandu Advocacy Forum KAGAF, muna da wakilai a kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi masu akida na son ci gaban matasa da kuma ilimi wanda shi ne dalili da ya hada mu da su.

Saboda haka zakulo marasa karfi irina bai yi mana wahala ba saboda muna da manufa iri daya da su.
Da farko mun shirya bayar da Form 260 yanzu kuma sun zama 320 duk wanda ya sami damar amfana da wannan Form kungiya ta dauki nauyin a cika mashi kyauta.

Samaila Mabo, ya bayar da kyautar FORM guda 50, Alh Zayyanu ya kara bayar da guda 10 Wanda aka hada da adadin farko 260 suka Zama 320.
An gudanar da taron a dakin taro na Royal Event Arena da ke Gwadangaji a jihar Kebbi.

Taron ya sami halartar manyan mutane da yan siyasa a fadin jihar Kebbi.

Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da:
Hon. Umar Altine Suru
Alh. Kabiru Giant
Alh. Zayyanu Sanka
Alh. Sagir Muhammad
da kuma  Alh. Bello O.G.
Wasu matasa da suka amfana da wadannan Form sun hada da:
Bello Abdulkadir, 
Mudassir Isah Fakara daga karamar hukumar Fakai.
Khadijat Musa
Tukur Sani Fasara
Bello Abdulkadir
da Faruku Aliyu,Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN