Kuma dai a Kebbi: Yan bindiga sun sake halaka mutum 13 sun sace shanu 500 a Danko-Wasagu


Yan bindiga sun sake kai wani farmaki a karamar hukumar Danko-Wasagu suka yi sanadin haka mutane 13 daga bisani suka sace shanaye kimanin 500 ranar Alhamis 8 ga watan Aprilu bayan farmakin ranar Laraba 7 ga watan Aprilu da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 7 da fararen hula 7.

Mun samo cewa da misalin karfe 4 na yammacin ranar Alhamis Yan bindigan da suka fito ta yankin Malekachi a karamar hukumar Mariga a jihar Niger da ke iyaka da jihar Kebbi, sun shigo ta Bakin Gulbi suka shiga garin Ayu suka shiga kauye da ke yankin kasar Kanya, suka yi ta harbe harbe, suka kora shanaye fiye da 500 a kauyuka da ke tsakanin Ayu da da Kanya.

Mun samo cewa Yan bindigan sun yi sanadin mutuwar mutane 13 a farmakin satar shanu tsakanin garuruwan Ayu,  Muzaba, Matseri, Dutsen Kuma, da sauran garuruwa da ke yankin, suka tattara shanu tare da farmakin jama'a kafin su kora shanun.

Wannan lamari ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 13, ciki har da Yan sa Kai da bayin Allah, tare da asarar shanu kimanin 500. Sai dai a wannan farmakin na Alhamis ba jami'in tsaro da ya rasa ransa.

Tsakanin ranar Laraba, Alhamis, zuwa safiyar ranar Juma'a, an yi zargin cewa soji 3, yansanda 4 da fararen hula 7 sun mutu. Kazalika mutum 13 sun mutu a farmakin ranar Alhamis, Wanda ya bayar da adadin mutuwar mutum 27 a cikin awa 24 kacal.

Majiyar mu ta ce tuni tawagar manyan jami'an Gwamnatin jihar Kebbi ta isa Masarautar Zuru tun ranar Alhamis, kuma ta zarce zuwa karamar hukumar Danko-Wasagu da sanyin safiyar Juma'a inda ziyarci wurare da wasu garuruwa da lamarin ya faru.

Masarautar Zuru, musamman karamar hukumar Danko-Wasagu da ke kudancin jihar Kebbi, ta tsunduma cikin mumunar matsalar tabarbarewan tsato, lamari da ya yi sanadin mutuwan bayin Allah da dama, tare da asarar dukiya, dabbobi da amfanin gona.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN