Jerin sabbabbin Jami’o’i 20 da hukumar NUC ta ba rajista da kuma Jihohin da su ka fito


A ranar Alhamis ne hukumar NUC mai lura da sha’anin jami’o’i a Najeriya ta ba wasu sababbin jami’o’i 20 na ‘yan kasuwa lasisin aiki a kasar nan.

Wadannan jami’o’i da aka kafa sun samu amincewar majalisar zartarwa ta kasa watau FEC.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, a cikin wadannan jami’o’in, babu wanda gwamnatin tarayya ko ta jiha ta mallaka, duk na ‘yan kasuwa ne.

Lasisin da aka ba wadannan sababbin jami’o’i ya kara adadin manyan makarantun da ake da su a Najeriya. Yanzu akwai jami’o’i 193 a fadin Najeriya.

Ga jerin wadannan jami’oi 20 nan kamar haka:

1. Jami’ar Topfaith, Mkpatak, (jihar Akwa Ibom)

2. Jami’ar Thomas Adewumi, Oko-Irese (jihar Kwara)

3. Jami’ar Maranatha, Mgbidi, (jihar Imo)

4. Jami’ar Ave Maria, Piyanko, (jihar Nasarawa)

5. Jami’ar Al-Istiqama, Sumaila, (jihar Kano)

6. Jami’ar Mudiame, Irrua, (jihar Edo)

7. Jami’ar Havilla, Nde-Ikom, (jihar Cross River)

8. Jami’ar Claretian of Nigeria, Nekede, (jihar Imo)

9. Jami’ar NOK, Kachia, (jihar Kaduna)

10. Jami’ar Karl-Kumm, Vom, (jihar Filato)

Mafi yawan jami’o’in nan su na yankin Arewacin kasar nan ne, daga cikin sababbin jami’o’in da aka kafa, jihohin Imo da Kwara sun samu makarantu biyu.

Kano na cikin jihar da ta fi cin ribar wannan kari da aka samu inda aka samu lasisin kafa jami’o’i uku: Al-Istiqama, Maryam Abacha da kuma ta Capital City.

Haka zalika an samu karin sababbin jami’o’i uku a Kwara, a Pategi, Offa da kuma garin Oko-Irese.

11. Jami’ar James Hope (jihar Legas)

12. Jami’ar Maryam Abacha (jihar Kano)

13. Jami’ar Capital City (jihar Kano)

14. Jami’ar Ahman, Pategi (jihar Kwara)

15. Jami’ar Offa, (jihar Kwara)

16. Jami’ar Mewar, Masaka, (jihar Nasarawa)

17. Jami’ar Edusoko, Bida, (jihar Neja)

18. Jami’ar Philomath, Kuje, (Abuja)

19. Jami’ar Khadija, Majia, (jihar Jigawa)

20. Jami’ar Anan, Kwall, (jihar Filato)

Za a ga cewa Jihohin Nasarawa da Filato a Arewa maso tsakiya sun tsira da karin sababbin jami’o’i biyu.

Source: Legit.ng News


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN