Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi


Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci daga gudanar da wa'azi har sai baba-ta-gani saboda zargin wuce gona da iri a karatunsa.

Dakatarwan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da kwamishinan al'amuran addini na jihar, Ahmad Jalam, ya sakawa hannu.

A jikin wasiƙar an saka adireshin Malam Abubakar Idris, Azare, ƙaramar hukumar Katagum , jihar Bauchi.

A wasiƙar wadda akai wa take da: "Karya doka da rashin ɗa'a ga dokar wa'azi a jihar Bauchi" an gano malamin na caccakar sahabban Annabi Muhammad (SAW) a cikin wa'azinsa.

Gwamnatin tace kalaman malamin ka iya jawo ruɗani tsakanin jama'a kuma zai iya sa mutane su karya doka a faɗin jihar.

Bisa wannan dalilin ne gwamnati ta dakatar dashi gudanar da wa'azi a faɗin jihar.

Wasiƙar tace:

"Gwamnatin jihar Bauchi ta gano wasu kalamanka da wa'azin ka, rahoto ya nuna cewa kana batanci ga sahabban Annabi Muhammad SAW a cikin wa'azinka."

"Wannan a bayyane yake, ɗabi'ar yin hakan ya saɓa ma dokokin wa'azi a jihar mu, kalamanka ka iya harzuƙa mutane kuma hakan na iya jawo rikici, gwamnati ba zata amince da haka ba."

"Saboda waɗannan dalilai, mun dakatar da kai daga gudanar da wa'azi da kuma jagorantar sallar jumu'a domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar mu."

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN