Type Here to Get Search Results !

Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaɓen Shekarar 2023


Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, INEC, ta sanar da cewa a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun ne za a yi zaben shekarar 2023 a kasar.

Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron yini guda da aka gudanar don sauraron laifukan zabe na 2021 da kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.

A cewar shugaban na INEC, saura shekara daya da watanni tara da makonnin biyu da kwana shida ko kuma kwanaki 660 a yi zaben daga yau.

"Kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanada, zaben zai kasance a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, ya rage saura shekara guda da watanni tara da sati biyu da kwanaki shida ko kwanaki 660 daga yau."

"Muna fatan za mu fitar da jadawalin zaben da zarar an kammala zaben gwamna na jihar Anambra wanda za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2021.

"Don yin hakan, ya dace a samu tabbaci kan tsarin dokokin zabe don gudanar da zaben. Muna fatan Majalisar Tarayya za ta yi abin da ya dace a cikin lokaci," in ji Farfesa Yakubu.

Yakubu ya ce daya daga cikin ayyukan da hukumar ke yi shine gurfanar da wadanda suka saba dokokin zabe, wanda ya ce shine mafi wahala a cikin ayyukan INEC.

Ya koka da cewa rashin gurfanar da wadanda suka saba dokokin zabe cikin lokaci shine babban kallubalen da hukumar ke fama da shi tun kafuwarta.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Source: Legit.ng News


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies