Da Ɗumi-Ɗumi: An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisa saboda barazanar tsaro


An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisar ƙasar nan saboda jami'an tsaro na ɗaukar dogon lokaci suna bincikar abubuwan hawan dake ƙoƙarin shiga harabar zauren.

Binciken abubuwan hawa a yau ya zarta na kowanne rana wanda hakan ya haddasa dogon layi a hanyar shiga zauren majalisar, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Ma'aikatan wurin da kuma yan jarida suna bata lokaci mai tsawo kafin su sami damar shiga zauren.

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai zargin barazanar tsaro wanda yasa dole aka tsaurara bincike kafin shiga zauren majalisar.

Ƙasar dai na fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da; ta'addanci a yankin arewa maso gabas, yan bindiga a yankin arewa maso yamma, rikicin makiyaya a yankin kudu maso yamma da sauransu.

A farkon makonnan ne, gwamnan Neja, Abubakar Bello, yace babban birnin ƙasar nan shima bai tsira ba bayan mayaƙan Boko Haram sun anshe iko da wasu kauyuka a Neja. Jihar Neja dai ta haɗa iyaka da birnin tarayya Abuja.

Hakanan kuma, a ranar Talata, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi taimakon kasar Amurka wajen yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.

A ranar Laraba, majalisar wakilai ta ƙaddamar da kwamitin mutane 40 domin su gano hanyoyin da za'a warware matsalolin tsaron da ƙasar nan ke fama dasu.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN