Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci daga gudanar da wa'azi har sai baba-ta-gani saboda zargin wuce gona da iri a karatunsa.
Dakatarwan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da kwamishinan al'amuran addini na jihar, Ahmad Jalam, ya sakawa hannu.
A jikin wasiƙar an saka adireshin Malam Abubakar Idris, Azare, ƙaramar hukumar Katagum , jihar Bauchi.
A wasiƙar wadda akai wa take da: "Karya doka da rashin ɗa'a ga dokar wa'azi a jihar Bauchi" an gano malamin na caccakar sahabban Annabi Muhammad (SAW) a cikin wa'azinsa.
Gwamnatin tace kalaman malamin ka iya jawo ruÉ—ani tsakanin jama'a kuma zai iya sa mutane su karya doka a faÉ—in jihar.
Bisa wannan dalilin ne gwamnati ta dakatar dashi gudanar da wa'azi a faÉ—in jihar.
Wasiƙar tace:
"Gwamnatin jihar Bauchi ta gano wasu kalamanka da wa'azin ka, rahoto ya nuna cewa kana batanci ga sahabban Annabi Muhammad SAW a cikin wa'azinka."
"Wannan a bayyane yake, ɗabi'ar yin hakan ya saɓa ma dokokin wa'azi a jihar mu, kalamanka ka iya harzuƙa mutane kuma hakan na iya jawo rikici, gwamnati ba zata amince da haka ba."
"Saboda waÉ—annan dalilai, mun dakatar da kai daga gudanar da wa'azi da kuma jagorantar sallar jumu'a domin tabbatar da zaman lafiya a faÉ—in jihar mu."
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari