Karin bayani: Farmakin Yan bindiga a Sakaba, DPO, Safeto 1, Mopol 7 da yan sa kai 2 ne suka mutu


Sabbin alkalumman adadin jami'an tsaro da suka mutu a farmakin Yan daban daji a yankin Makuku da kewaye a karamar hukumar Sakaba da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi ya nuna DPO na ofishin yansandan Sakaba, Safeton yansanda daya, yansandan kwantar da tarzoma 7 da Yan sa Kai biyu ne aka tabbatar da mutuwarsa.

Idan baku manta ba, alkalumman farko a daren Lahadi sun nuna karancin adadin mamata sabanin sabbin alkalumman da suka fito yau Litinin 26/4/2021, kamar yadda Kakakin rundunar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya tabbatar.


Jami'an tsaron sun rasa rayukansu ne lokacin da suke kokarin kare dukiya da rayukan al'umma ta hanyar fuskantar Yan daban dajin da suka tafka mumunan ta'asa bayan sun sace shanaye bayin Allah kimanin 1000.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN