Jami'an tsaro sun kashe Ikonso, kwamandan IPOB, mashiryin hare-hare a kudu


Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya da takwarorinsu na rundunar soji da farin kaya, a wani aikin hadin guiwa da suka yi a sa'o'in farko na ranar Asabar, sun tsinkayi hedkwatar 'yan ta'addan IPOB dake kauyen Awomama dake karamar hukumar Oru ta gabas a jihar Imo inda suka halaka 'yan tada kayar baya.

'Yan ta'addan ne suke da alhakin kai hari hedkwatar 'yan sandan jihar da gidan gyaran hali a ranar 5 ga watan Afirilun 2021.

Sun kai wasu jerin farmaki ga jami'an tsaro da wurare da suke a yankunan kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan.

Rahotannin sirri da PRNigeria ta samu ta llllllllllllllllllll da cewa jami'an tsaro sun tunkari sansanin 'yan ta'addan inda tsagerun suka dinga sakar musu ruwan wuta.

"Cike da kwarewa da zakakuranci, rundunar tsaron hadin guiwan suka yi martani. Daga bisani sun halaka gagararren kwamandan IPOB na kudu maso gabas da aka fi sani da Ikonso tare da wasu mayaka masu makamai.

"An san kwamanda Ikonso a matsayin mataimakin shugaban kungiyar kuma mai shugabantar ayyukan tsageranci na kungiyar. Shine mashiryin harin hedkwatar 'yan sandan Imo da kuma sauran wuraren jami'an tsaro.

"Aikin na daga cikin kokarin 'yan sandan da sauran jami'an tsaro wurin shawo kan ta'addanci a jihohin kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan," majiyar tace.

Bayan artabun ruwan wuta, jami'an tsaro sun samu gawar Ikonso kwamanda da wasu mayaka 6. An samu miyagun makamai masu tarin yawa da suka hada da AK47, daruruwan harsasai, layu da sauransu.

A yayin rubuta wannan rahoton, 'yan sanda uku da soja daya suna karbar taimakon masana lafiya sakamakon miyagun raunikan da suka samu yayin musayar wutar.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN