Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta damke wani matashi da yayi sanadin mutuwar wani dattijo mai shekaru 60 kuma mahaifin abokinsa bayan ya lakada masa mugun duka. Jaridar legit ta ruwaito.
Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin a yammacin Talata.
Lamarin ya faru ne a unguwar sheka dake birnin Kano sakamakon takaddamar da ta hada matashin da mahaifin abokinsa.
A cewar Kiyawa, samun bayanin aukuwar lamarin ce tasa suka garzaya wurin kuma likitoci ne suka tabbatar da mutuwar dattijon.
Dattijon mai suna sale Usman yana zaune a wurin sana'arsa yayin da matashin ya sheke shi.
Duk da dai dan marigayin yace babu wata rashin jituwa tsakaninsu, don haka bai san dalilin matashin na yin haka.
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari