Allah ya yi wa Sayyada Rabi'atu Harun, matar da ta yi fiice wajen wakokin yabon Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ta riga mu gidan gaskiya. Jaridar legit ta ruwaito.
BBC ta ruwaito cewa mijinta, Sharif Mu'az ya ce ta rasu ne a ranar Talata 16 ga watan Maris a Rigasa Kaduna bayan jinya na makonni uku.
An yi jana'izarta bisa koyarwar addinin musulunci a yammacin ranar Talata kamar yadda mijinta ya bayyana.
Sharif Mu'az ya ce ya yi matkukar girgiza sakamakon rasuwar matarsa da ya bayyana a matsayin mutumiya mai hali na gari kana ya yi addu'ar Allah ya jikanta da rahama.
Marigayiyar ta rasu ta bar 'ya'ya biyu a duniya.
Cikin wakokin da ta yi na yabon annabi akwai 'Mai daraja Annabi Ma'aiki', Zahra'u Fadima, Shukriyya Sajida, Sayyidin Nasi Karimi da sauransu.
Jama'a da dama masu son wakokinta da sauran musulmi sun yi jimamin rasuwarta a dandalin sada zumunta inda suka yi addu'ar Allah ya jikanta da rahama ya gafarta mata.
Wani mai amfani da shafin Twitter Isa Usman ya yi alhinin rasuwar Sayyada Rabi'atu yana mai addu'ar Allah ya jikanta ya yi mata rahama ya karbi bakuncinta domin darajar Annabi Muhammadu Rasulullah.
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari