Wata uwargida ta kashe Amaryar mijinta mai suna Fatima yar asalin jihar Katsina bayan ta banka mata wuta har ta mutu.
Lamarin ya faru ne ranar Talata 23 ga watan Maris kimanin makonni bakwai bayan aurensu da mijinta dan jihar Niger.
Wani dan uwan Amaryar ya gaya wa Katsina post cewa Uwargida da Amarya basu zaune a gida daya.
Sai dai Uwargida ta yi tattaki har gidan da Amarya take zaune kasancewa babu nisa daga gidan da take, ta yi mata dan karen duka har ta galabaita, daga bisani ta kulle ta a cikin daki kuma ta banka wa gidan wuta har Amarya ta kone ta mutu a cikin gobarar.
Za a yi janaizan Amarya a gidansu da ke Sabuwar Unguwa a cikin birnin Katsina ranar Laraba 24 ga watan Maris.
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari