Type Here to Get Search Results !

Gwamnan Ebonyi ya ce yan kudu sun fi more shekara 5 da Buhari ya yi bisa shekara 16 na PDP


Mai girma gwamnan jihar Ebonyi, Mista David Umahi ya fito ya yi wasu kalamai da za su iya fusata babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da ya baro. Jaridar legit ta wallafa.

Gwamna David Umahi ya bayyana cewa mutanen kudu maso gabas sun fi morar gwamnati Muhammadu Buhari a kan sauran gwamnatocin PDP.

Jaridar Vanguard ta ce David Umahi ya bayyana wannan ne ta bakin kwamishinan yada labarai da wayar da kan al’ummar jihar Ebonyi, Orji Uchenna Orji.

Barr. Orji Uchenna Orji ya ce mutanen Kudu maso gabas sun fi cin moriyar gwamnatin APC ta fuskar tattalin arziki da samun abubuwan more rayuwa.

A cewar gwamnatin Ebonyi, daga cikin romon da yankin ya samu a mulkin Muhammadu Buhari akwai:

1. Gyaran filin tashi da saukar jirgin sama na Naira biliyan 10

2. Aikin gadar Neja ta biyu.

3. Hanyar Enugu zuwa Fatakwal

da sauransu

Dave Umahi ya cigaba da cewa:

“Wadannan alamu ne da cewa gwamnatin nan ta taimaka wa mutanen Kudu maso gabas fiye a kowa.”

Dazu kun ji cewa PDP ba ta dandara da 2019 ba, ana kishin-kishin za a ba Atiku Abubakar da Peter Obi tutar jam’iyya da nufin karbe mulki daga hannun jam'iyyar APC.

Wata majiya ta ce akwai yiwuwar PDP ta sake ba Atiku/Peter Obi tikitin kujerar Shugaban kasa.

Wasu manyan jam’iyyar hamayyar su na da ra’ayin shugaba Muhammadu Buhari bai lashe zaben 2019, don haka ake ganin Atiku zai iya doke duk wanda APC ta tsaida.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies