Kisan Abba Abbey: An kama tsohuwar masoyiyarsa da saurayinta


Rundunar yansandan jihar Sokoto ta kama tsohuwar masoyiyar marigayi Abba Abbey Gidan Haki bisa zargin kasancewa wacce ta kitsa kashe shi saboda wata bukata, Jaridar Daily trust ta ruwaito.

An Sami gawar Dan shekara 50 a Duniya kuma mahaifin yara 5 yashe a gefen titin zuwa garin Durbawa a karamar hukumar Kware ranar 19 ga watan Maris bayan an sace shi ranar 18 ga watan Maris.

Daily trust ta samo cewa tsohuwar masoyiyar Abba Abbey ce ta ci amanarshi bisa sabbin bayanai da suka bayyana.

Rahotun ya ce suna dab da yin aure ne sai kuma lamarin bai wakana ba amma suka ci gaba da hulda.

Wata majiya daga yansanda ta shaida wa Daily trust cewa ta tsohuwar masoyiyarsa ta hada baki ne da sabon masoyin ta domin ta sami kudin aurenta da shi daga wajen Abba. Sakamakon haka suka hada baki aka sace shi. Bayan sun gano cewa baya da kudi, sai suka kashe shi.

Rahotun ya yi zargin cewa bayan wadanda suka sace shi sun gano baya da kudi, sai suka gaya wa tsohuwar masoyiyarsa cewa su za su kashe shi. Sakamakon haka suka je wajen da suka daure shi suka bi ta kansa da mota.

Yanzu haka tsohuwar masoyiyarsa tare da sabon masoyinta suna hannun yansanda, kuma yansanda sun sami bindiga kirar AK47 a wajensu.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE