Sojin Najeriya sun yi zanga zangan kan rashin isassun makamai


Sojojin rundunar Operation Lafiya Dole sun gudanar da zanga-zanga kan turasu faggen yaki da 'yan ta'addan Boko Haram. Jaridar legit ta ruwaito.

A cewar majiyoyi daga barikin Maimalari, Sojojin sun mamaye hedkwatar Operation Lafiya Dole ne a daren Alhamis suna harbin bindiga sama.

Sun bayyana cewa suna zanga-zanga ne sakamakon rashin biyansu alawus da kuma rashin isassun makaman yaki.

A jawabin wasu daga cikin sojojin da suka bukaci a sakaye sunayensu, sun bayyana yadda yan ta'addan Boko Haram suka hallaka Sojoji a harin Marte saboda makaman yan ta'addan sun fi nasu.

Channels TV ta bayyana cewa kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Isa Ado, ya tabbatar da labarin.

Wannan zanga-zanga na Soji ya biyo bayan fallasan da NSA Babagana Munguno yayi cewa an nemi kudin makamai an rasa karkashin tsaffin hafsoshin tsaro.

Mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta'addan Boko Haram.

NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma'a, 12 ga Maris.

Amma mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shehu ya bayyana hakan a shirin Politics Today na ChannelsTV ranar Juma'a inda yace kudi $1billion da aka saki a 2018 don sayen makamai, an yi amfani da su.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN