NNPC ya ce za a koma saida litar man fetur a kan N234 a gidajen mai


Shugaban kamfanin mai na kasa na NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce gwamnati ta na biyan N100n-N120b a matsayin kudin tallafin fetur duk wata. Jaridar legit ta ruwaito.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban na NNPC ya na cewa ba za su iya cigaba da bada tallafi domin gidajen mai su rike farashin lita a N162 ba.

Ya ce: “NNPC kadai ke shigo da fetur. Mu na sayen mai a farashin kasuwa, mu saida a N162. Ya kamata lita ta kai tsakanin N211 da N234 a gidan mai.”

Wannan yunkuri da gwamnatin tarayya ta ke yi na taba kudin man fetur ba zai yi wa al’umma dadi ba, don haka kungiyoyin kwadago su ka sa damara.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba a wata hira da ya yi, ya ce jama’a ba za su iya karbar wani karin kudi a halin tsadar kaya da rashin aikin yi da ake ciki ba.

Wabba yake cewa baya ga tsadar rayuwa, annobar COVID-19 ta jikkata mutanen Najeriya, sannan ga matsin lambar tattalin arzikin da ake fuskanta a kasa.

Amma NNPC ta na ganin babu abin da zai hana farashin fetur tashi. Mele Kyari yake cewa idan aka duba za a ga Najeriya ta fi makwabtanta arahar mai.

Masana su na ganin ya kamata gwamnatin tarayya da NNPC su rika yin gaskiya wajen bayyana wa Duniya abin da ake batar wa da sunan tallafin man fetur.

Wasu na ganin a maimakon a rika kashe Naira biliyan 120 duk wata wajen rage tsadar fetur, zai fi kyau ayi amfani da kudin nan a wajen ayyukan more rayuwa.

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani bayan wani taro da aka yi a fadar Aso Villa, kun ji cewa Mele Kolo Kyari ya koka da cewa ba za a iya cigaba da tafiya a haka ba.

Injiniya Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa kudin da ake kashe wa wajen tace litar danyen mai, sannan ayi dakonsa zuwa Najeriya ya na tashi ne a kan N234.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN