Limamin babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi Imam Abdullahi Muhktar (Walin Gwandu) ya bukaci al'umma su taimaka wa jami'an tsaro a jihar Kebbi wajen tafiyar da aikin inganta tsaro, sakamakon binciken ababen hawa da ke dauke da bakin glass, rashin ingantattun takardu da lambar mota, wanda jami'an tsaro ke gudanarwa yanzu haka a garin Birnin kebbi.
Imam Muhktar ya yi wannan bukatar ne a Hudubarsa kafin gabatar da Sallar Juma'a a Central Mosque da ke Birnin kebbi ranar Juma'a 26 ga watan Maris.
Daga cikin Hudubarsa, Imam Muhkatar ya ce:
"Hakika al'amarin bakin glass na motoci ya wajaba a hana shi tun daga kampuna da suke yin shi da kampuna da suke sayar da shi, da kuma hana motoci sanya shi domin abu ne mai zaburar da shakku da rashin aminci da tuhuma idan mutane suka gani.
Saboda haka nike Kiran jama'a su tashi tsaye su taimaki jami'an tsaro, taimako mai karfi, ga duk abin da ke taimakawa a kare rayuwa , dukiya da tsaron jama'a. Domin samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Idan muka yi wasa da wannan, za mu fuskanci hatsari da damuwa mai yawa da akiba mai ban tsoro a Duniya da lahira.
A karshe, ina kira ga ma'abuta ingantattun hankulla da lafiyayyun zukata cewa, ku kasance tare da jami'an tsaron ku domin hana wadannan miyagun dabi'u da kuma miyagun harkoki. Ku tashi tsaye don ku tsira, kuma ku tserar da iyalanku , abokanku, yanuwanku, kasar ku, da jama'a baki daya. Kuma ku kasance da jami'an tsaro wajen hana aikata laifi ko ta'addanci ga mutane da basu ji basu gani ba .
A karshe, muna rokon Allah madaukaki ya yi mana afuwa, ya bamu lafiya Duniya da lahira". Inji Imam Abdullahi Muhktar (Walin Gwandu).
Fadakarwa daga Central Mosque Rt. Hon Hassan Muhammad Shallah, Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kebbi ya dauki nauyi. Allah ya saka masa da alkhairi. Amin.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka