Type Here to Get Search Results !

Kebbi: Matashi ya kashe babban Limamin garin Saminaka, matar aure da makwabcinsa


Ana zargin wani mutum da ake zargi da tabin hankali ya kashe babban Limamin Masallacin garin Saminaka, tare da matar kanin babanshi wacce take dauke da tsohon ciki, da makwabcin su, a karamar hukumar Shanga da ke kudancin jihar Kebbi a tarayyar Najeriya ranar Asabar 20 ga watan Maris.

Ana zargin cewa wanda aka kama ya yi amfani da gatari da itace wajen kashe wadannan bayin Allah.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka Yan Banga a garin Saminaka sun cafke wanda ake zargi amma jama'an gari sun yi alam baram cewa sai an mika masu shi domin su dauki fansa.

A daidai lokacin da muke rubuta wannan rahotu, mun sami tabbacin cewa babban jami'in dansanda DPO na garin Saminaka, yana iya kokarinsa tare da Hakimin garin wanda tun farko ya yi tsaye domin ganin ba a kashe wanda ake zargi ba kafin isowar DPO..

Karin bayani anjima....
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies