Babban bankin Najeriya (CBN) ya ninka kuɗaɗen da aka ware don tallafawa magidanta da masu ƙananan sana'o'i (TCF) daga 150 biliyan zuws 300 Biliyan. Jaridar legit ta ruwaito.
Tsarin na TCF wanda aka sake buɗewa kwanan nan na bada rancen kuɗi ga magidanta da masu ƙananan san'o'i waɗan da annobar korona ta shafa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana haka yayin buɗe taron ƙarama juna sani karo na 30 da bankin ke shirya ma masu kula da sha'anin kuɗi wanda ya gudana ta fasahar zamani (Virtually).
Gwaman wanda mataimakinsa akan ayyukan kamfanoni, Adamu Lamtek, ya wakilta yace ya zuwa yanzun an rabar da kuɗaɗe N149.21 biliyan ga mutane 316,869, saboda haka ne ma aka ninka kuɗin don 'yan Najeriya da dama su amfani da shirin.
A cewarsa wannan shirin da gwamnati ta ɓullo dashi zai ƙara yawan hada-hadar kuɗi a cikin ƙasa wanda hakan ka iya haɓɓaka tattalin arziƙin Najeriya.
Ya ce: "An yanke wannan hukunci ne saboda karuwar mutane da suke bukata, kuma wannan shiri ana cike shi ne ta yanar gizo, baya ɗaukar wani lokaci wajen cikewa."
Ya yin da yake martani kan maganganun ɗake yawo cewa CBN ya canza matsayarsa akan hada-hadar kuɗin yanar gizo 'Cryptocurrency' Gwamnan yace: "CBN bata bada wata sabuwar doka akan kuɗin ba, kowa yasan matsayar mu akan kasuwancin, kuma bamu canza ba."
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka