Wani Bafulatani ya harbi kansa da karamar bindigar hannu kirar gida a goshinsa a wata Ruga da ke garin Bunza da ke jihar Kebbi ta tsakkya a tarayyar Najeriya ranar Juma'a 19 ga watan Maris.
Rahotannin farko sun yi zargin cewa Bafulatanin yana wasa da bindigar ne a Rugarsu, daga bisani tsautsayi ya sa bindigar ta tashi bayan ya auna kansa a goshi da zafin rana bayan Sallar Juma'a.
Mun samo cewa jami'an yansanda jihar Kebbi reshen Bunza, sun kai wa Bafulatanin dauki, suka garzaya zuwa Asibitin garin Bunza da shi.
Sai dai mun tattaro cewa, ana zargin cewa an tura shi zuwa babban Asibitin koyarwa ta UDUTH da ke Sokoto domin samun wadataccen kulawan kwararrun Likitoci.
Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yansanda na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari