Kebbi: Gurnanin Dan Bagudu ya sa Yan sa Kai sun shiga buya a garin Zuru


Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya fara kakkabe burbushin rashin kunya da ta'addanci da wasu bata gari ke yi da sunan aikin sa Kai a garin Zuru da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.

Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo cewa zancen nan da ake yi, babu ragowar ko mutum daya da za ka gani dauke da guntun gatari da ake alakantawa da gatarin tsafi, bindigar wagila ko kananan bindigogi, adduna ko kulake da sunan Sa Kai a cikin garin Zuru.

Lamari da ya tsabtace tunanin zanan lafiya tare da inganta tsaro tsakanin jama'a a cikin garin Zuru bisa ra'ayin Yusuf Sani mazauni unguwar Zango a cikin garin. Zuru.

Bincike da muka gudanar kan lamarin ya nuna cewa bayan an yi zargin cewa Yan sa Kai sun yi wa Alhaji Mande Kanya kisan wulakanci kuma suka yi ma wani Lauya dukan Allah ya isa, wata majiya daga mahukuntan jihar Kebbi ta yi barazanar cewa ranar ta'addanci da sunan sa Kai a kasar Zuru ta zo karshe.

Mun tattaro cewa mahukunta a jihar Kebbi, sun yi wa lamarin diran kamun kaji, inda aka tura daruruwan jami'an tsaro suka dinga tsabtace garin Zuru daga mutane da ke dauke da makamai suna addaban jama'a da sunan sa Kai marmakin fuskantar yan bindiga da ke addaban al'umma a yankin Bena da ke da iyaka da jihar Zamfara daga bangaren jihar Kebbi.

Kazalika mun samo cewa yanzu haka a cikin garin Zuru, ba wanda zai yi ikirarin cewa shi dan sa kai ne. Mun samo cewa , yayin da yan sa kai suka shiga buya a garin Zuru, akwai sauransu a kauyuka da ke ci gaba da taimaka wa jami'an tsaro wajen dakile hare haren yan bindiga a yankunan karkara.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE