An kama kwarto turmi da tabarya tare da matar aure, duba abin da miji ya aikata


An kashe wani mutum mai suna Johane Mareya bayan an kama shi yana lalata da wata matar aure a gidanta, sakamakon haka mijin matar ya kashe shi nan take.

Dan shekara 27 mijin matar mai suna Oscar Mazorodze, dan asalin kauyen Chirindagomo, a Chief Chireya da ke Gokwe ta Arewa a kasar Zimbabwe, ya fada hannu kuma aka gurfanar da shi a gaban Alkalin Kotun Majistare Mai suna Busani Sibanda, a garin Gokwe bisa zargin kashe Mareya. 

An yi zargin cewa  ranar 5 ga watan Maris, Mazorodze ya bar wajen aiki da wuri kuma ya dawo gida da misalin karfe 3 na rana, amma ya tarar da an rufe kofar daki daga ciki, sai ya banke kofar kuma ya wuce zuwa cikin kuryar daki, inda ya yi ido biyu da Mareya yana lalata da matarsa Brenda Dhlodhlo tsirara turmi tabarya. Nan take ya dauki wukar aikin gida na mata ya dinga caka  wa Mareya a ko ta ina a jikinsa. 

Makwabta da suka ji karar rigima da ake yi a gidan, sun kai Mareya Asibitin garin Gokwe, inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Mai shari'a Busani Sibanda, ya tasa keyar Mazorodze zuwa Kurkuku har zuwa ranar 19 ga watan Maris, kuma ya shawarce shi cewa zai iya neman beli a babban Kotu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN