Type Here to Get Search Results !

Kebbi: Yan bindiga sun farmaki Gulumbe da Nayelwa, sun dauke matar Magajin gari


Da misalin karfe daya na daren Juma'a Yan bindiga sun shiga gidan Magajin garin Nayelwa suka yi awon gaba da daya daga cikin matarsa, a karamar hukumar Kalgo da ke jihar Kebbi ta tsakiya ranar 19 ga watan Maris.

Magajin garin Nayelwa Muhammed Kabir Usman, ya shaida wa manema labarai cewa Yan bindigan sun shigo gidansa ne dauke da muggan makamai cikin dare. 

Ya ce bayan Yan bindigan basu gan shi ba, sai suka dauke daya daga cikin matarsa suka tafi da ita. Ya ce Yan bindigan sun bar lambar wayarsu kafin su tafi.

A wani labarin na daban, mun samo cewa wasu mutane kimanin su 8 dauke da makamai, sun farmaki wasu mutane Yan asalin Gulumbe a wani waje da ke rikon Kardi a cikin daren Juma'a.

Rahotanni sun ce wasu mutane kimanin su 8 dauke da makamai da suka hada da adduna, kulake da sauransu, sun farmaki wasu mutum biyu da ke tafiya a kan babur da dare a wata hanyar daji. Kawai sai suka far masu da sara da duka.

Mun samo cewa daya daga cikin wanda ke kan babur ya samu ya tsere, amma sai maharan suka sassare ragowar dayan wanda aka garzaya zuwa Asibiti Sir Yahaya da shi.

Karin labari anjima...Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies