Ka fito da hujjar da za ta nunawa Duniya Fulani sun kai maka hari - Inji kungiyar Arewa


Kungiyar Arewa Youth Federation (AYF) ta jefa wa gwamnan jihar Benuwai, Mista Samuel Ortom, kalubale a game da harin da ya ke cewa an kai masa. Jaridar legit ta ruwaito.

Arewa Youth Federation ta bukaci gwamna Samuel Ortom ya fito da hujjojin da za su nuna makiyaya Fulani ne su ka kai masa hari a ranar Asabar.

Samuel Ortom ya fito ya fada wa Duniya Fulani ne su ka nemi su ga karshen rayuwarsa, ya ce ‘yan Miyetti Allah Kautal sun yi barazanar ganin bayansa.

Amma shugaban kungiyar Arewa Youth Federation, Adamu Kabir Matazu, ya na da ta-cewa a game da wannan ikirari da Mai girma Samuel Ortom ya yi.

Daily Trust ta rahoto Alhaji Adamu Kabir Matazu ya na mamakin yadda Ortom ya cin ma wannan matsaya.

Matazu ya ce: “Mun ga hare-hare a kan gwamnoni kamar lokacin da aka ga ‘Yan Boko Haram sun kai wa tawagar gwamnan Borno, Babagana Zulum hari.”

A game da harin da ake cewa an kai wa Zulum, Adamu Kabir Matazu, ya ce babu wata hujja a kasa.

Shugaban na Arewa Youth Federation ya ce akwai shakku game da batun kai wa gwamnan hari, ballatana a daura laifin a kan Fulani ba tare da wata hujja ba.

“Amma Ortom bai gabatar da wasu hujjoji ba. Ana samun bata-gari a kowane bangare a al’umma, babu hujjar da ke nuna an kai masa hari, har ma ace makiyaya Fulani ne.”

Kun samu labarin cewa wata kungiyar Fulani ta fito ta yi ikirarin ita ce ta kai wa gwamnan jihar Benuwai Benuwai hari, ta ce ta so ne ta hallaka Samuel Ortom.

FUNAM mai rajin kare muradin Fulani ta ce alhakin yunkurin kashe Gwamna Samuel Ortom ya na kanta, dalilinta shi ne gwamnan ya na adawa da kabilar.

Kungiyar ta ce: “Duk inda kuka kasance, matukar kun nuna wa Fulani adawa, za mu durkushe ku."


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN