Mai gadin makaranta mai shekara 60 ya yi wa marainiya yar shekara 10 fyade


Mazauna Graceland Avenue, da ke karamar hukumar Osisioma Ngwa a jihar Abia, sun yi ma wani tsoho dan shekara 60 duka kuma suka zagaya da shi a unguwa bisa zargin yi wa yarinya marainiya yar shekara 10 fyade.

Rahotanni sun ce wannan tsoho ya lallashi yarinyar ne ta shiga dakinsa, daga bisani ya yi mata fyade a asirce kuma ya bukaci kada ta gaya wa kowa.

Yarinyar tana zaune tare da mahaifinta  tare da kannenta su biyu bayan rasuwar mahaifiyar.

Mun samo cewa tsohon da aka fi sani da suna "Mbaise" Mai gadi ne a wata makarantar sakandare da ke Unguwar.

Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda mahaifin yarinyar ya ki amincewa ya kai kara wajen yansanda.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN